
Katsina
Muna bukatar agajin gaggawa daga Gwamnatin tarayya kan tsaro
Mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Farouk Lawal Jobe, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta ɗaukar matakai na musamman wajen kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da suka ƙara ta’azzara a jihar.
Wannan roƙo na zuwa ne bayan wani mummunar harin da aka kai wa al’ummar Mantau, karamar hukumar Malumfashi, inda ’yan bindiga suka kashe mutane 13 a masallaci yayin da suke salla da safiyar Talata.
Nagarifmradio