Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Taraiya ta goge shafukan sada zumunta sama da miliyan 13 saboda kalaman cin zarafi

Gwamnatin Taraiya ta goge shafukan sada zumunta sama da miliyan 13 saboda kalaman cin zarafi 

Gwamnatin ta ce ta goge shafukan ne daga kafafen sada zumunta da su ka haÉ—a da Facebook, Tiktok, Instagram, X da sauran su.

Daraktan sashin yaɗa labarai ma hukumar Cigaban Sadarwa da Fasahar Zamani ta ƙasa, NITDA, Hajiya Hadiza Umar, a wata sanarwar da ta fitar a yau Laraba, ta ce an goge shafuka miliyan 58,909,112 kawo yanzu.

Ta ce hakan ya biyo bayan karya dokokin sadarwa ta ƙasa.

Ta kuma yabawa Google da Tiktok bisa bin dokoki da ƙa'idojin gwamnatin Nijeriya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)