Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara 6 a gidan yari

Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara 6 a gidan yariĀ 

Kotu ta PƤijƤt-HƤme da ke Finland ta yanke wa Simon Ekpa, mai rajin kafa ʙasar Biyafara, hukuncin shekara shida a gidan yari kan laifukan ta’addanci.

Kotun ta same shi da laifin tayar da zaune-tsaye da kuma shiga cikin ayyukan ʙungiyar ta’addanci.

A cewar jaridar YLE ta Finland, kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi amfani da ā€œyawan mabiyan da yake da su a kafafen sada zumuntaā€ wajen hura tarzoma a yankin kudu maso gabashin Najeriya tsakanin watan Agustan 2021 da Nuwamban 2024.

Kotun ta kuma gano cewa Ekpa babban jigo ne a wata ʙungiyar ā€˜yan a ware masu ɗaukar makami, wadda burinta shi ne raba Najeriya don kafa ʙasar Biyafara.

Haka kuma kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya samar wa wasu ʙungiyoyi makamai, bama-bamai da harsasai ā€œta hanyarĀ  sadarwa da yake da ita a yankinā€, sannan an kuma same shi da laifin ʙarfafa mabiyansa a dandalin sada zumunta na X da su aikata laifuka a Najeriya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)