
Yan bindiga sun kashe mutane biyu kauyen Dudaye, karamar hukumar Augie a jahar Kebbi.
Maudu’i Korafi Kan Matsalar Tsaro a Karamar Hukumar AugiuÂ
‎
‎Mai Girma Gwamna,Â
‎
‎Ina rubuto wannan takarda ne don nuna matukar damuwa da bakin ciki game da halin rashin tsaro da ake fuskanta a Karamar Hukumar Augie. Lamarin ya kai wani mataki mai tayar da hankali, musamman da yawaitar hare-haren 'yan bindiga da sace-sacen mutane.Â
‎
‎Wani Al’amari na Musamman:
‎A ranar 30 ga Agusta, 2025, a kauyen Dudaye, mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga.Â
‎
‎Tasirin Lamarin
‎Mutane da dama sun bar gidajensuÂ
‎Harkokin kasuwanci sun tsaya cikÂ
‎Tsoro da firgici sun mamaye zukatan jama'aÂ
Nagarifmradio