Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya,
Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya, a wani hari da suka kai kan wasu mutane da suka koma garinsu daga sansanin ƴan gudun hijira, a jiya Asabar.
Â
Harin ya auku ne a daren ranar Juma'a, a garin Darul-Jama a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, garin da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.
Â
Wata majiya ta shaida wa ƴan jaroda cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin guda 55, har da sojoji guda biyar, da kuma wani ɗan sa-kai guda ɗaya.
Â
Mazauna yankin sun ce mayaƙan sun ƙaddamar musu da harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka ce maharan sun kutsa garin ne a kan babura ɗauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi, sannan suka riƙa ƙone gidaje.