MayaĆan Boko Haram sun kashe aĆalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya,
- By NAGARIFMNEWS --
- Sunday, 07 Sep, 2025

- 266 views
MayaĆan Boko Haram sun kashe aĆalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya, a wani hari da suka kai kan wasu mutane da suka koma garinsu daga sansanin Ć´an gudun hijira, a jiya Asabar.
Â
Harin ya auku ne a daren ranar Juma'a, a garin Darul-Jama a Ćaramar hukumar Bama ta jihar Borno, garin da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.
Â
Wata majiya ta shaida wa ƴan jaroda cewa daga cikin waÉanda aka kashe Éin guda 55, har da sojoji guda biyar, da kuma wani Éan sa-kai guda Éaya.
Â
Mazauna yankin sun ce mayaĆan sun Ćaddamar musu da harin ne da misalin Ćarfe 8:30 na dare, inda suka ce maharan sun kutsa garin ne a kan babura Éauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi, sannan suka riĆa Ćone gidaje.




