
Shugaba Tinubu zai kai ziyara Kaduna ranar Juma’a
Shugaba Tinubu zai kai ziyara Kaduna ranar Juma’a
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa Kaduna a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025 domin ziyarar aiki ta yini ɗaya.
A cewar wata sanarwa daga mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shugaban zai halarci bikin ɗaurin aure tsakanin Nasirudeen Yari, ɗan Sanata Abdul’aziz Yari (Zamfara ta Yamma), da Safiyya Shehu Idris.
Bayan haka, Shugaba Tinubu zai kai ziyara ta girmamawa ga Hajiya Aisha Buhari, matar marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a gidansu da ke Kaduna.
Ana sa ran shugaban kasa zai koma Abuja a daren ranar Juma’a bayan kammala ziyarar.
Nagarifmradio