Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Ce “Muna Maraba da Duk Abin da Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro”
- By NAGARIFMNEWS --
- Friday, 26 Dec, 2025

- 26 views
Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Ce “Muna Maraba da Duk Abin da Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro”
Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa tana maraba da duk wani yunƙuri ko haɗin gwiwa da zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
A wata sanarwa da Ofishin Gwamnatin Sokoto ya fitar, gwamnatin ta jaddada cewa batun tsaro ba wai na gwamnati kaɗai bane, har ma shi ne na kowa da kowa, domin ya shafi rayuka da dukiyoyin al’umma baki ɗaya.
Sanarwar ta ce jihar ta sha fama da kalubale iri‑iri na rashin tsaro, ciki har da hare‑haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane, amma gwamnati na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kan wannan matsala.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba da gudunmawa ta hanyar bayar da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro, tare da zama masu kula da lafiyar unguwanni da yankunansu.
A cewar gwamnatin jihar, haɗin kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro shi ne mabuɗin kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Sokoto.
Allah ya ba da nasara wajen kare rayuka da dukiyoyi kuma ya ba da zaman lafiya a yankin baki ɗaya.
Nagarifmradio




