Za a gudanar da taron tsaro na musamman a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi, a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025. Taron zai mayar da hankali ne kan tattauna hanyoyin da za su kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, tare da tsohon Hafsan Sojojin Najeriya kuma tsohon Ministan Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (Rtd), za su jagoranci wannan muhimmin taro.
Shugaban Arewa Broadcast Media Practitioners Forum, Alhaji Yelwa, ya bayyana cewa taron zai tattaro gwamnonin Arewa, masana tsaro, da sauran manyan jami’an gwamnati domin tattauna dabarun samar da mafita mai dorewa ga matsalar tsaro.
Ya ce babban burin taron shi ne kafa ingantaccen dandamali na tattaunawa da hadin gwiwa domin dawo da zaman lafiya, karfafa amincewar jama’a ga hukumomin tsaro, tare da yaki da tsattsauran ra’ayi a yankin.
Nagarifmradio