Dakarun hadin gwiwa na rundunonin tsaro (JTF) da ke Faruruwa sun kubutar da wani bawan Allah da aka sace a kan iyakar jihohin Katsina da Kano.

Dakarun hadin gwiwa na rundunonin tsaro (JTF) da ke Faruruwa sun kubutar da wani bawan Allah da aka sace a kan iyakar jihohin Katsina da Kano. 

Da asubar fari ta yau Lahadi dakarun suka kai farmaki yankin bayan sun samu wasu bayanan sirri masu tushe game da mmotsin yan bindiga daga yankunan Daurawa da Kira na Jihar Katsina zuwa Kano.

A cewar Jami’in Hulada da Jama’a na Birged na uku na runudnar sojin kasa ta Najeriya, Manjo Babatunde Zubairu , nan take dakarun da ke Sansanin Bakin Daga na Yankwada suka nufi kan iyakar don dakile yan ta’addar.

Manjo Zubairu ya kara da cewa dakarun tsaron sun yi arba da yan bindigar ne a Ungwan Dogo da Ungwan Tudu inda aka yi dauki ba dadi.

Ya kuma ce bayan da suka ji wuta ta yi wuta yan bindigar sun tartwatse in da suka tsere hajaran majaran zuwa Karamar hukumar Matazu ta Jihar Katsina.

Yayin farmakin ne, a cewar mai magana da yawun sojojin, aka ceto mutumin da aka sace din mai shekara 38 da haihuwa wanda aka ce yan bindugar sun harbe shi a kafa lokacin da suka dauke shi.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)