Madugun jam’iyyar NNPP kuma tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya amince da tsayar da ’ya’yan wasu daga cikin ’yan majalisar dokokin jihar Kano da suka rasu, domin su tsaya takara a matsayin wakilan iyayensu.

Rahotanni daga Aminiya sun bayyana cewa ’yan takarar sun haɗa da Aminu Sa’ad (Halifa) da Nabil Aliyu Daneji, waɗanda za su tsaya takara a mazabar Ungoggo da ta Birni, domin maye gurbin iyayensu da suka rasu kwanan nan.

Kwankwaso ya ce wannan mataki na daga cikin yunƙurin jam’iyyar na ci gaba da wakiltar al’umma cikin kwanciyar hankali da kuma girmama gudunmuwar da waɗanda suka rasu suka bayar tun da fari.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)