Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba.
- By NAGARIFMNEWS --
- Monday, 29 Dec, 2025

- 13 views
’Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Gebbe a Jihar Kebbi, An Rasa Rayuka da Dama.
Wasu ’yan bindiga sun kai mummunan hari a garin Gebbe, da ke Ward ɗin Gebbe, Ƙaramar Hukumar Shanga a Jihar Kebbi, inda ake zargin sun kashe mutane da dama tare da jefa al’umma cikin firgici.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya faru ne ba zato ba tsammani, inda ’yan bindigar suka shiga garin suna harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa jama’a da dama tserewa zuwa dazuka da garuruwa makwabta domin tsira da rayukansu.
Wata majiya ta ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, yayin da ake fargabar cewa asarar na iya ƙaruwa sakamakon tsananin harin.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa a hukumance daga rundunar tsaro ko gwamnatin Jihar Kebbi ba dangane da faruwar lamarin, sai dai ana sa ran jami’an tsaro za su kai ɗauki yankin domin dawo da zaman lafiya.
Mazauna garin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Nagarifmradio




