Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu biyar suka makale a ƙarƙashin gine-ginen da ya rushe a wata masana’antar sarrafa shinkafa da ke Jihar Kebbi.
- By NAGARIFMNEWS --
- Wednesday, 31 Dec, 2025

- 40 views
Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu biyar suka makale a ƙarƙashin gine-ginen da ya rushe a wata masana’antar sarrafa shinkafa da ke Jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a lokacin da wani ɓangare na ginin ya ruguzo, inda ya rutsa da wasu ma’aikata da ke ciki. Zuwa lokacin da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, ana ci gaba da aikin ceto don kubutar da waɗanda suka makale.
Hukumomin gaggawa da jami’an tsaro na ci gaba da aiki tare da ‘yan agaji, domin tabbatar da cewa an ceto sauran mutanen da ke karkashin ginin cikin koshin lafiya.
An fara bincike domin gano musabbabin rushewar ginin.
Nagarifmradio