Kabar shagala a turai kadawo gida Yan Najeriya na shan wahala - ATIKU

Atiku ya zargi Tinubu da rashin kulawa da mutanen Najeriya yayin da suke fuskantar mummunan yanayin tsaro, yana mai cewa ya zauna a Turai yana shagala. 

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi suka mai tsanani game da yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanar da harkokin tsaro a kasar, inda ya zarge shi da rashin kasancewa da rashin kulawa yayin da kasar ke fuskantar mummunan yanayi.

 

A cikin wata sanarwa mai zafi da ya fitar a shafinsa na Facebook, Atiku ya yi tir da gazawar gwamnatin Tinubu wajen magance hare-haren da suka faru a Jihar Benue, wanda suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a  Logo da Gbagir a Karamar Hukumar Ukum.

 

"Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da cewa tana da gaskiya, rashin kwarewa, da kuma rashin tsari na daukar matakai wajen magance matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a Najeriya," in ji Atiku. "Wannan ba kawai ra'ayina ba ne - amma kuma yana zama ra'ayin shugabannin adawa, kwararru a fannin tsaro,  hatta wasu daga cikin mambobin jam'iyyar mulki sun gamsu da gazawar Gwamnati"

 

Ya nuna bakin ciki game da yadda shugaban kasar bai nuna damuwa ko jagoranci a lokacin da ake fuskantar matsaloli a kasar ba. 

 

"Jinin marasa laifi na ci gaba da zuba a Najeriya cikin rashin tausayi... Amma gwamnatin Tinubu tana ci gaba da rashin kulawa, ba ta nuna gaggawa ko kuma kima ga farfadowar al'umma," in ji Atiku.

 

Ya kwatanta shugabannin duniya da suka kasance cikin kasarsu a lokacin matsaloli da faruwar bala'o'i, inda ya ambaci misalan Shugaban Amurka Barack Obama, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, da kuma tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wadanda suka dawo gida domin jagoranci a lokacin da ake bukatar su.

 

"Amma Shugaba Bola Tinubu... ya zabi tafiya zuwa Turai, yana gudanar da Najeriya daga nesa kamar yana hutu. Idan ba zai iya daukar mataki ba, Abu mafi sauki da zai iya yi shi ne ya bayyana," in ji Atiku.


Comment As:

Comment (0)