Seyi Tinubu Ya Kai Matsayin Da Zai Nemi Takara A Kowane Irin Muƙamin Siyasa A Nijeriya Ciki Har Da Kujerar Shugaban Ƙasa, Inji Daniel Bwala

Seyi Tinubu Ya Kai Matsayin Da Zai Nemi Takara A Kowane Irin Muƙamin Siyasa A Nijeriya Ciki Har Da Kujerar Shugaban Ƙasa, Inji Daniel Bwala

Mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman, Daniel Bwala ya caccaki masu sukar shugaba Bola Tinubu cewa ya na shirin kafa ɗan sa Sheyi ya tsaya takarar gwamna a jihar Legas. 

A wani shirin rediyo na yanar-gizo a shafin 'Clarity Zone' a ranar Laraba, Bwala ya ce ai ba laifi ba ne idan Sheyi ya nemi takara ko ma ta shugaban ƙasa ce, inda ya ce doka ta baiwa Sheyi dama ya tsaya takara ko da Tinubu ne a 2027 ballantana ta gwamna a Legas.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)