Majalisar Dattawa ta buÉ—e ofishin Sanata Natasha, ta ba ta damar shiga harabar Majalisar.

Majalisar Dattawa ta buÉ—e ofishin Sanata Natasha, ta ba ta damar shiga harabar Majalisar.

A ranar Talata, rahotanni sun nuna cewa rikicin da ke tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na jam’iyyar PDP daga Kogi ta Tsakiya da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya fara samun sauƙi.

An bayyana cewa majalisar ta cire Takunkumin da aka sa a ofishin Sanata Natasha tare da ba ta cikakken damar shiga harabar Majalisar Dokoki ta Ƙasa (NASS). 

Wannan mataki ya nuna cewa ana neman kawo ƙarshen takaddamar da ta haifar da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.

Duk da cewa cikakkun bayanai kan yadda aka cimma matsayar ba su fito fili ba tukuna.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)