
Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta karyata zarge-zargen Malami, ta ce ba su da tushe kuma siyasa ce kawai
Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta karyata zarge-zargen Malami, ta ce ba su da tushe kuma siyasa ce kawai
Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta karyata zarge-zargen da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya yi, inda ya zargi Gwamna Nasir Idris da shigo da ’yan daba da mayaƙa na haya cikin jihar.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Asabar, Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Muhammad Usman, ya ce waɗannan zarge-zarge na da nufin tayar da hankali da kuma ɓata suna gwamnatin da mutanen Kebbi gaba ɗaya.
Ya ce: *“Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zama lafiya a Najeriya. Duk wani yunkuri na ɓata wannan suna, ba wai kan gwamna kawai ne ba, har da mutanenmu gaba ɗaya.”*
Abubakar Malami, wanda ke jagorantar jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, ya rubuta takardar ƙorafi a ranar 10 ga Satumba, 2025, zuwa ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Darakta Janar na DSS, da kuma Kwamptrola Janar na Hukumar Shige da Fice da ta Civil Defence, inda ya zargi wasu manyan ’yan siyasa da haɗin gwiwa da mayaƙa daga Jamhuriyar Nijar, suna shigo da makamai ta haramtattun hanyoyi.
Nagarifmradio