Za mu tura Tinubu zuwa gida Lagos a 2027: Inji Malam Nasir El rufa i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya sha alwashin cewa gamayyar jam’iyyun adawa za su kayar da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.

Da yake jawabi yayin wani taron Arewa Tech Fest karo na biyu da ya gudana a jihar Katsina, El-Rufai ya ce za su sauke Tinubu, yayin da za su ci gaba da aiki da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Bosun Tijani a gwamnati mai zuwa.

Tsohon gwamnan kuma jigo a jam’iyyar SDP ya ce Bosun Tijjani yana aiki mai kyau don haka za su ci gaba da aiki tare da shi


Comment As:

Comment (0)