Siyasar

2027: NNPP za ta tattauna kan yiwuwar marawa Tinubu baya ko shiga kawancen jam'iyyun adawa a taron ta na koli

2027: NNPP za ta tattauna kan yiwuwar marawa Tinubu baya ko shiga kawancen jam'iyyun adawa a taron ta na koli 

Jam’iyyar NNPP na shirin yanke hukunci kan muhimman abubuwa a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da za ta gudanar a ranar Alhamis, 28 ga Agusta, 2025 a birnin Abuja. 

Jaridar Tribune ta rawaito cewa alamomi sun nuna za a ɗauki manyan matakai a wannan taro yayin da jam’iyyar ke tsara dabaru gabannin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson, ya fitar, an bayyana cewa taron zai tattauna kan babban taron jam’iyya, duba zaɓen cike gurbi na baya-bayan nan, da kuma tattauna dabarun wayar da kan jama’a tare da shirin ƙara wa’adi na rajistar sababbin mambobi. Haka kuma, jam’iyyar za ta yi nazari kan sauye-sauyen kundin tsarin mulki da ake yi yanzu domin gabatar da matsayinta kan muhimman batutuwa don kare dimokuraɗiyyar ƙasar.

Sai dai sanarwar ta yi karin haske cewa, duk da jita-jita a bainar jama’a ko sharhin ‘yan siyasa kan irin shirin da ake yi na zaɓen 2027, jam’iyyar na nan daram kan manufofi da ƙimomin da aka kafa ta a kai, tare da kasancewa a buɗe ga wasu canje-canjen siyasa masu tasiri. Sanarwar ta ƙara da cewa akwai yiwuwar NNPP ta goyi bayan neman tazarce na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

“Musamman game da jita-jitar da masu sharhi da ra’ayin jama’a ke yadawa kan inda NNPP ta dosa kafin babban zaɓen 2027, muna nan kan matsayar da muka sha faɗa.

“Wannan kuwa shi ne cewa siyasa abu ne a bude amma dole ne aikace-aikacenmu da shawarar da muke ɗauka su kasance sun daidaita da ƙa’idodinmu da manufofin mu. Haka kuma batun maslahar ƙasa yana da muhimmanci.

“A kan haka, NNPP Kofar ta a buɗe take da zaɓuɓɓuka guda uku da muka ambata a baya: haɗa kawance ko yin gamayya, ci gaba da zama NNPP mai zaman kanta domin shiga zaɓe, ko kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu don tazarce.

“Za a tattauna waɗannan zaɓuɓɓukan uku a taron NEC da za mu yi ranar 28 ga watan Agusta, 2025. Don haka muna kira ga dukkan mambobinmu su kasance cikin natsuwa, domin duk wata shawara da za a ɗauka za ta kasance don maslahar al’umma,” in ji sanarwar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)