Rundunar 'yan sanda sun bukaci sanata Mr La ya gurfana a gaban su kan Barazana Ga Rayuwa Gwamna Uba sani.

Rundunar 'yan sanda sun bukaci sanata Mr La ya gurfana a gaban su kan Barazana Ga Rayuwa  Gwamna Uba sani.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce ta samu ƙorafi daga ofishin Ma’aikatar Shari’a na jihar bisa umarnin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, inda ake zargin Sanata Lawal Adamu Usman da aikata laifuka da suka shafi barazana ga rayuwa da kuma yaɗa ƙarya masu cutarwa akan gwamnan.

A cikin takardar gayyata da kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Rabiu Muhammad (psc, mni) ya sanyawa hannu, an umarci Sanata Lawal Adamu Usman da ya bayyana a gaban kwamishinan ‘yan sanda na Kaduna a ranar Litinin, 1 ga Satumba, 2025, domin ya amsa waɗannan zarge-zarge.

Kwamishinan ya ce hadin kai daga bangaren sanatan zai kasance abin godiya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)