Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar, duk da cewa a shirye yake ga tattaunawa da sauran shugabannin siyasa.

Yayin da yake jawabi a Abuja, a wajen taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) na NNPP karo na tara, Kwankwaso ya karyata jita-jitar da ke cewa yana shirin sauya sheka.
Ya ce:
“Wasu da dama sun yi zaton yau za mu sanar da ko zan zauna a NNPP ko zan koma wata jam’iyya ko kuma na hada kai da wasu mutane. Amma ba hakan ne manufar taron ba. Muna da jam’iyyarmu, kuma muna cikin nishadi da farin ciki.”
Ya kara da cewa, duk da cewa jam’iyyar ba ta cikin tafiyar gaggawa, tana da sassauci tare da kasancewa a bude ga tattaunawa.
“Muna da yakinin cewa muna da abin da za mu bayar a matakin jagoranci mafi girma na wannan kasa. Mun shirya yin magana da kowa, amma duk wata tattaunawa za ta kasance ta hadin gwiwa,” in ji shi.
Nagarifmradio