
Siyasar kano
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta sanar da kori ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa,
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta sanar da kori ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin ayyukan da suka saba wa jam’iyya da kuma kasa cika wajibin kuɗaɗen da ya rataya a wuyansa ga jam’iyyar.
Shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, wanda ya bayyana haka yayin jawabi ga manema labarai a Kano ranar Asabar, ya ce matakin ya biyo bayan kalaman da Jibrin ke yi a kafofin watsa labarai kan jam’iyyar da shugabanninta.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan lamari ya faru ne cikin sa’o’i 24 bayan ɗan majalisar ya bayyana cewa bai kamata a yi mamaki ba idan ya fice daga jam’iyyar.
Ya kuma ce ya isa girma don ya ɗauki matsaya da kansa kan abin da ya fi masa amfani a siyasance.
Da yake mayar da martani, Dungurawa ya bayyana Jibrin a matsayin “ɗan siyasa marar ƙarfi” wanda nasarar da ya samu a zaɓe ta faru ne kawai saboda goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya da kuma jam’iyyar NNPP, ba wai ƙarfin kansa ba.