
Sanata Natasah Za Ta Koma Zauren Majalissar Dattijan Najeriya Gadan-gadan
Sanata Natasah Za Ta Koma Zauren Majalissar Dattijan Najeriya Gadan-gadanÂ
Senata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, za ta koma Majalisar Dattawan Najeriya a ƙarshen wannan wata bayan kammala dakatarwarta ta tsawon watanni shida.
Lauyanta, Victor Giwa ne ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa, za ta ci gaba da gudanar da aikinta na wakiltar al’ummarta a zauren majalisar kamar yadda doka ta tanada.
Akpoti-Uduaghan, wadda ta lashe kujerar majalisar a zaben 2023, ta fuskanci dakatarwa ne a baya sakamakon wasu dalilai da majalisar ta bayyana a wancan lokaci, in ji News Direct.
Ana sa ran dawowarta za ta ƙara ba wa mazaɓarta murya da tasiri a muhimman muhawara da shawarwarin da suka shafi ci gaban ƙasa da yankin Kogi ta Tsakiya.
Nagarifmradio