Yau Gwamnatin tarayya ta yaye askarawa 819 na Jahar Kebbi da zasu kula da dazuzukan kasar nan.
- By NAGARIFMNEWS --
- Saturday, 27 Dec, 2025

- 35 views
Yau Gwamnatin tarayya ta yaye askarawa 819 na Jahar Kebbi da zasu kula da dazuzukan kasar nan.
Mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi Sanata Umar Tafida yayi kira ga sarakunan gargajiya da su taimaka musu wurin gudanar da aikinsu ta hanyar basu baya nan sirrri.
Hakama Mai Ba shugaban kasa shawara kan harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Yan sanda Umar Hadejia yace askarawan zaa bazasu dazuzuka nan take.
Ya ce an koya musu dubarun yaki, kuma zaa basu bindiga kirar AK-47 domin aiwatar da aikinsu.
Askarawan 819 sun fito daga kanannan hukumomin Arewa, Augi, Dandi da Kuma Danko-Wasagu.
Nagarifmradio




