
'Yadda Marigayi Abba Kyari Ya ba Mu Cin Hanci ni da Rimi': Sule Lamido Ya Yi BankaÉ—a
Kamar Yadda Legit Hausa ta wallafa ashafinta Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi wata bankaÉ—a kan marigayi Abba Kyari. Lamido ya ce shi da marigayi Abubakar Rimi sun Æ™i karÉ“ar cin hancin N160m daga Kyari domin samun goyon bayan su wajen zama mataimakin Olusegun Obasanjo.Â
Â
Lamido ya yi magana kan Abba Kyari Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wani bangare na littafinsa mai suna 'Being True to Myself', cewar PunchÂ
Â
Lamido ya kaddamar da littafin ne a ranar 13 ga Mayun 2025 da muke ciki a birnin Tarayya, Abuja. Tsohon ministan ya ce waÉ—anda ake tunanin ba su mukamin sun haÉ—a da Jibril Aminu, Adamu Ciroma, da Abubakar Rimi.Â
Â
Sule Lamido ya ce Kyari, wanda daga baya ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa a zamanin Muhammadu Buhari, ya zo da takardar banki ta N160m. A babi na tara, 'Abdulsalami’s Transition and Formation of the PDP', Lamido ya ce Kyari ya bar wajen cikin kunya bayan sun ƙi karɓar kuɗin da ya kawo musu.