
An Samu Wanda Zai Buga da Tinubu, Jigo Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa a APC
FCT Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar APC a 2019, Cif Charles Udeogaranya, ya sake dawowa da nufin takara a zaɓen 2027. Jigon APC ya yi watsi da matakin da jam'iyyar APC ta ɗauka na bai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tikitin tazarce ba tare da hamayya ba.
Udeogaranya ya yi fatali da wannan matakin, ya ce babu batun nuna fifiko da ƙarfa-ƙarfa a tsarin dimukuraɗiyya, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Ɗan siyasar ya yi wannan furuci ne bayan goyon bayan da shugabannin APC, gwamnoni da 'yan majalisar dokoki suka bai wa Shugaba Bola Tinubu a Taron Koli na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.
APC ta sami ɗan takarar da zai kara da Tinubu A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Udeogaranya ya ce: “Babu wata doka a tsarinmu da ta tanadi bayar da tikiti kai tsaye babu hamayya ga wani ɗan takara. Zan tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a 2027.”
Jigon jam'iyya mai mulki ya kara da cewa babu zancen fitar da ɗan takara ta masalaha ko a ce kowa ya aminta da shi a irin wannan halin da ƙasar nan take ciki, rahoton Daily Post.