
Kungiyar FOMWAN Ta Bayarda Tallafi Ga Marayu Dake Daukacin Masarautun Gwandu Da Argungu.
Kungiyar FOMWAN Ta Bayarda Tallafi Ga Marayu Dake Daukacin Masarautun Gwandu Da Argungu.
Â
A wani mataki na saukaka wa al'umma musamman marayun acikin wannan wata mai alfarma, kungiyar Mata ta FOMWAN Reshen wannan jaha ta kaddamar da tallafin kudi ga marayun dake Masarautun Gwandu da Argungu.
Â
Da take jawabi a wurin taron, Amirar kungiyar Hajiya Balkisu Zaki ta bayyana muhimmancin taimakon marayu tareda gargadi game da cin dukiyar marayu, inda tace a irin wannan lokaci da Marayu ke budar ido yakamata al'umma subada tasu gudumuwa wajen sanya farin Ciki a zukatansu.
Â
Hakama ta kara da cewa nan bada jimawa ba kungiyar tasu zata kaddamarda irin wannan tallafi ga sauran marayun dake masarautu biyu wato Yauri da kuma Zuru.
Â
Itama da ta ke jawabi shugabar mata ta sashen jinkai da walwala ta FOMWAN ta yi kira da jan kunne ga iyayen da marayun suke karkashin kulawar su da suyi anfani da kudin yadda ya da ce.
Â
Akallah marayu 100 ne suka samu tallafin naira 10,000 daga masarautar gwandu yayin da a garin argungu marayu 50 ne suka samu tallafin naira 5000.
FOMWAN