An buÉ—e cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da wata cibiyar bai wa almajirai da yara mata marasa zuwa makaranta ilimin kwamfuta da na sana'o'i "domin inganta rayuwarsu".
Cibiyar wadda gwamnatin ta gina tare da tallafin asusun tallafa wa yara na duniya UNICEF, zai mayar da hankali wajen koya wa É—aliban ilimin yadda za su yi sana'a ta amfani da fasahar zamani, ta hanyar amfani da wayoyin hannu da kuma kwamfuta.
Manufar shirin ita ce tallafa wa tsarin bayar da ilimi ga kowa, a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Â
Baya ga ilimin kwamfuta, É—aliban za su kwashe shekara É—aya suna samun horo a sana'o'i daban-daban da kuma ilimin rubutu da karatu.
Sokoto na cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar yawaitar yara marasa zuwa makaranta da kuma almajirai masu gararamba a kan tituna.
A ƙarshen shekarar 2024, gwamnatin jihar ta bayyana cewa kimanin yara 800,000 ne suka yi rajista a makarantu, lamarin da ya nuna ci gaba a ɓangaren idan aka kwatanta da shekarun baya.